Harkar noma: Mun ci nasara matuka - Inji Shugaba Buhari

Harkar noma: Mun ci nasara matuka - Inji Shugaba Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin sa ta samu nasara a bangaren noma domin kuwa yanzu an daina shigo da kashi 90% na shinkafa kamar yadda aka saba a baya.

Harkar noma: Mun ci nasara matuka - Inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace Gwamnatin sa za ta kara dagewa wajen noma
Source: Depositphotos

Shugaba Muhammadu Buhari yayi wannan bayani ne kwanakin baya a Daura lokacin da ya tafi hutu inda ya ke cewa duk da kokarin Gwamnatin sa, wasu masu fasa-kauri na cigaba da shigo da shinkafa musamman ta Yankin Kasar Benin a boye.

A jawabin Shugaban kasar, yace za a karya masu cigaba da shigo da kayan abinci a boye cikin Najeriya domin kuwa zai yi bakin-kokari wajen ganin shinkafa ta kara araha. Shugaban kasar yace yanzu dai jama’a duk sun koma gona a kasar.

KU KARANTA: Yadda Gwamnatin Buhari ke kokarin samawa Talakawa gidaje a Najeriya

Shugaban kasar yace komawa gonar da aka yi za ta taimakawa jama’a da ke dogaro da wasu, ya zama sun yi hobbasa sun tashi. Buhari yace yanzu har ta kai Ma’aikatan Gwamnati sun fara kakkabe gonakin gado domin a samu kayan abinci.

Kamar yadda wannan sako ya zo mana, Shugaba Buhari ya nuna cewa babu abin da ke tsananin damun sa a Najeriya kamar ya ga wasu sun rasa abinci har ta kai su na dogaro da wasu. Shugaban yace yanzu dai an karfafa harkar noma a Najeriya.

Jama’a dai sun fara nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zai iya yin biyu-babu a zaben 2019. Bukola Saraki dai zai nemi takarar Shugaban kasa ya rabu da kujerar Sanatan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel