Ambaliyar ruwa ya lalata gidaje sama da 5,000 a Sokoto, Kebbi da Zamfara - NEMA

Ambaliyar ruwa ya lalata gidaje sama da 5,000 a Sokoto, Kebbi da Zamfara - NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa NEMA) ta bayyana cewa sama da gidaje 5,000 ne suka halaka a kananan hukumomi 16 na Sokoto, Kebbi da Zamfara sakamakon ambaliyar ruwa a damunan wannan shekarar.

Shugaban kula da hukumar na Sokoto, Sulaiman Muhammad ya bayyana hakan a Gusau a ranar Alhamis yayin bude taron kwanaki uku na horar da jami’an hukumar da aka gudanar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa anyi horon ne domin yin garambawul da sake wayarwa ma’aikatan NEMA kai.

Ambaliyar ruwa ya lalata gidaje sama da 5,000 a Sokoto, Kebbi da Zamfara - NEMA

Ambaliyar ruwa ya lalata gidaje sama da 5,000 a Sokoto, Kebbi da Zamfara - NEMA
Source: Twitter

Mista Muhammad ya bayyana cewa kananan hukumomin da abun ya shafa sune Sabon-Birni, Kebbe, Tangaza, Goronyo, Wamakko da Illela a Sokoto; da ku Argungu, Maiyama, Birnin-Kebbi, Shanga, Bunza da Danko Wasagu a jihar Kebbi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku da magoya bayansa sun mamaye hedkwatar PDP

Ya bayyana cewa Maru, Tsafe da wasu yankunan karamar hukumar Gusau ma abun ya shafe su a jihar Zamfara.

Ya ja hankalin jama’a da su dunga lura da alamomin ambaliya a yankunansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel