Alhakin rashin aiki na yana kan Makiyayan da su ka addabi Benuwai – Gwamnan Jihar

Alhakin rashin aiki na yana kan Makiyayan da su ka addabi Benuwai – Gwamnan Jihar

Gwamnan Jihar Benuwai watau Samuel Ortom ya yanki fam din sake neman takara a kan kujerar sa. Wannan karo Ortom zai sa ran karawa ne a tsohuwar Jam’iyyar sa watau Jam’iyyar adawa ta PDP.

Alhakin rashin aiki na yana kan Makiyayan da su ka addabi Benuwai – Gwamnan Jihar

Gwamna Ortom ya zargi Makiyaya da hana Benuwai cigaba
Source: Depositphotos

Tuni har Gwamnan ya yanki fam din takara ya kuma cike har ya maida. A lokacin da Gwamnan ya mika takardun neman takarar sa a babban ofishin Jam'iyyar PDP ne ya bayyana cewa rikicin Makiyaya ya hana sa wasu ayyuka a Jihar.

Gwamnan ya zanta da ‘Yan jarida a babban Birnin Tarayya Abuja inda ya zargi ta’adin da Makiyaya su ka yi a Jihar Benuwai wajen hana Gwamnatin sa karasa wasu ayyuka da ta fara a fadin Jihar cikin shekaru 3 da yayi a kan mulki.

KU KARANTA: Kwankwaso ya bayyana babbar matsalar da ake fama da ita a Najeriya

Samuel Ortom ya koka da cewa har yanzu ba a iya shiga wasu Kauyuka a Benuwai saboda irin ta’adin da Makiyaya su kayi a Yankin. Wasu ma dai sun tsere daga irin wadannan wurare don haka aka gaza ayyukan da aka fara inji Gwamnan na PDP.

Duk da haka dai Gwamnan ya bayyana cewa ya gina dakunan karatu na Makarantun firamare fiye da 7000 a Jihar. Gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin wani babban Hadimin sa Abraham Kwanghngu kamar yadda mu ka samu labari a makon nan.

A baya Gwamnan ya zargi rikicin Makiyaya da jawowa Jihar rashin fiye da Naira Biliyan 400. Rikicin Makiyayan dai yayi kamari a wasu Garuruwa na Jihar inda aka rasa dukiya da rayuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel