Saraki ya caccaki kakakin jam’iyyar APC, ya kalubalance shi da suyi muhawara

Saraki ya caccaki kakakin jam’iyyar APC, ya kalubalance shi da suyi muhawara

Bayan sanarwar da aka alakanta da kakakin jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Nabena Yekinim, game da kudirin takaran shugabancin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya kalubalanci Nabena da zo suyi muhawara a ko wani tashar talbijin na kasa.

Ya kuma bayyana Nabena a matsayin mutun mutumi da aka kera don wasu dalilai, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Saraki ya fusata ne saboda an bayyana shi a matsayin mai rashawa, kuma babban mashiririci wadda ya gaza a harkokin shugabancin siyasa.

An rahoto cewa Nabena ya caccaki tsohon gwamnan na jihar Kwara, in da ya kara da cewa Saraki na takara ne domin ya janye hankulan mutane daga mnyan laifuka da rashawa da ake zargin sa akai.

Saraki ya caccaki kakakin jam’iyyar APC, ya kalubalance shi da suyi muhawara

Saraki ya caccaki kakakin jam’iyyar APC, ya kalubalance shi da suyi muhawara
Source: Depositphotos

Da yake mayar da martani ta babban mai bashi shawara akan shafukan zumunta da kafofin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu, Saraki yace ba zai bari furucin wani mutun dake abuja amma ake shirya masa jawabansa daga Lagas ya dame shi ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Wata kungiya na son siyawa Buhari fam din takara a matsayi tukwicin dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas

Sanata Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Buhari suna bala'in tsoron ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP na zaben 2019 mai zuwa.

Haka zalika fitaccen dan siyasar ya kuma ce yana kalubalantar jam'iyyar ya zuwa wata muhawarar keke-da-keke akan abubuwan da suka shafi kasar da al'ummar cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel