An garkame wasu Mutane 2 bisa laifin yiwa karamar Yarinya da wata Mata fyade a jihar Gombe

An garkame wasu Mutane 2 bisa laifin yiwa karamar Yarinya da wata Mata fyade a jihar Gombe

Wata Kotun majistire dake zamanta a jihar Gombe, ta bayar da umarnin garkame wasu biyu bisa laifin yiwa wata karamar yarinya 'yar shekara 4 da kuma wata Matashiya mai shekaru 25 fyade da ake zargin tana da tabuwar hankali.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, daya daga cikin wannan mutane biyu da ake zargi, Isiayaka Tajudden na unguwar Sabon Gari dake jihar Gombe, ya yiwa 'yar karamar yarinyar fyade da misalin karfe 7.00 na yammacin ranar 23 ga watan Yulin da ya gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin Tajuddeen da ya yiwa yarinyar ta karfi cikin wani daki inda ya keta ma ta haddi tare da cin zarafi ba tare da wani tausayi ko jin kanta ba.

An garkame wasu Mutane 2 bisa laifin yiwa karamar Yarinya da wata Mata fyade a jihar Gombe

An garkame wasu Mutane 2 bisa laifin yiwa karamar Yarinya da wata Mata fyade a jihar Gombe
Source: Twitter

Kazalika, wani matashi mai shekaru 21 na unguwar Barunde, Muhammad Bello, ya shiga hannun hukumar ne bisa laifin yaudarar wata Rukayya Hassan wajen murkushe ta tare da keta ma ta mutuncinta, sai dai ana zargin wannan Matashita na da tabin kwakwalwa.

KARANTA KUMA: Na bar N13bn a asusun ajiya na Gwamnatin Jihar Sakkwato - Bafarawa

Laifin wannan matasa biyu ya ci karo da sashe na 282 cikin dokokin kasar nan a yayin da jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu, Sufeto Bako Shakari, ya bayar da shaidar cewa kawowa yanzu hukumar na ci gaba da gudanar da bincike kan wannan mummunan lamari.

A sanadiyar haka Alkalin kotun, Mista Babayo Usamatu, ya daga sauraron karar zuwa ranakun 25 da kuma 27 na watan Satumba domin ci gaba da shari'ar tare da bayar da umarnin garkame matasan biyu a gidan kaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel