2019: Hada-hada ta barke a ofishin jam’iyyar APC na kasa

2019: Hada-hada ta barke a ofishin jam’iyyar APC na kasa

- Masu son yin takara na cigaba da yin tururuwa zuwa ofishin jam’iyyar APC na kasa domin sayen fam din tsayawa takara a zaben 2019

- Masu son yin takara karkashin inuwar jam’iyyar ta APC sun fara isa ofishinta na kasa da misalign karfe 8:00 na safiyar yau, Alhamis

- Wasu kungiyoyi biyu sun sayawa dan takarar gwamna a jihar Adamawa, Dakta Mahmood Ahmed, fam guda biyu

Masu son yin takara sun fara yin tururuwa zuwa ofishin jam’iyyar APC na kasa domin sayen fam dinsu na tsayawa takara a zabukan shekarar 2019 mai zuwa.

‘Yan takara a karkashin APC sun fara isa shelkwatar jam’iyyar ta kasa da misalign karfe 8:00 na safiyar yau, Alhamis.

A wani sabon salon siyasa, kungiyoyi biyu sun sayawa dan takarar gwamna a jihar Adamawa, Dakta Mahmood Ahmed, fam guda biyu tare da kai masa su har gidansa dake unguwar Maitama a Abuja.

2019: Hada-hada ta barke a ofishin jam’iyyar APC na kasa
Ofishin jam’iyyar APC
Asali: UGC

Da yake karbar fam din da kungiyoyin suka saya masa, Ahmed ya ce, “ina mika godiya ga abokaina da suka bani mamaki ta hanyar saya min fam din takara saboda maganar gaskiya na karaya bayan uwar jam’iyya ta fitar da farashin fam din takara.

DUBA WANNAN: 2019: An samu tashin tarzoma da hargitsi yayin da Atiku ya mayar da fam ofishin PDP

Mambobin jam’iyyar APC da dama sun yi korafi a kan tashin gwauron zabi da farashin fam din takarar kujeru daban-daban ya yi amma duk da hakan masu son yin takarar na ruge-rugen sayen fam dinsu na tsayawa takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel