Yanzu Yanzu: IGP yayi umurnin dakatar da jami’an yan sanda 3 dake da hannu a binciken gidan Edwin Clark

Yanzu Yanzu: IGP yayi umurnin dakatar da jami’an yan sanda 3 dake da hannu a binciken gidan Edwin Clark

- Babban sufeton yan sanda ya yi umurnin dakatar da jami’an yan sanda uku dake da hannu a birkice gidan Cif Edwin Clark

- Kakakin rundunar Jimoh Moshood ya bayyana hakan

- A yanzu haka za'a gurfanar da wanda ya kai tsegumn lamarin

Babban sufeton yan sanda ya yi umurnin dakatar da jami’an yan sanda uku dake da hannu a birkice gidan Cif Edwin Clark a Abuja ba bisa ka’ida ba.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da aka aikewa Legit.ng a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba daga kakakin rundunar, ACP Jimoh Moshood.

Yanzu Yanzu: IGP yayi umurnin dakatar da jami’an yan sanda 3 dake da hannu a binciken gidan Edwin Clark

Yanzu Yanzu: IGP yayi umurnin dakatar da jami’an yan sanda 3 dake da hannu a binciken gidan Edwin Clark
Source: Depositphotos

Jami’an uku sune: Inspekta Godwin Musam, Inspekta Sada Abubakar da kuma Inspekta Yabo Paul.

Cikon jami’i na hudun, David Dominic, mataimakin Suprtendent din yan sanda na karkashin bincike a cewar sanarwan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar 'yan sandan Najeriya ta kama wani Ismail Yakubu da ake zargi da bayar da bayannan karya da ya janyo jami'an yan sanda suka kai sumame gidan Cif Edwin Clark a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yanki fam din takaran shugaban kasa a APC

Yakubu mazaunin wani kauye ne mai suna Waru da ke Apo a babban birnin tarayya Abuja. Kakakin hukumar yan sanda, Jimoh Moshood, ya ce za'a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu a yau Laraba bisa tuhumarsa da laifin yiwa 'yan sanda karya.

Ya kuma kara da cewa jami'an 'yan sanda hudu da su kayi sumamen suna tsare har zuwa lokacin da za'a kammala bincike da Sufeta Janar na 'yan sanda ya bayar da umurnin da gudanar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel