An ceto mutane shida daga wani gida da ya rushe a Kano

An ceto mutane shida daga wani gida da ya rushe a Kano

- Anyi nasarar ceto mutane shida daga wani gida da ya rushe a jihar Kano

- Biyu cikin mutanen da aka ceto sun rasu, sauran hudun suna asibiti suna karbar magani

- Gidan ya rushe ne a daren ranar Laraba a Unguwar Gwammaja da ke birnin Kano

Jami'an kashe gobara sun ceto rayukkan wasu mutane shida da gini ya danne a yammacin jiya Laraba a Gwammaja da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobarar ta Kano, Saidu Mohammed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai (NAN) a ranar Alhamis cewa cikin wadanda aka ceto daga ginin har da wani yaro mai shekaru 10.

An ceto rayuwar mutane shida daga wani gida da ya rushe

An ceto rayuwar mutane shida daga wani gida da ya rushe
Source: Twitter

Mohammed ya cigaba da cewa, "mun samu kiran neman ceto ne misalin karfe 8.14 na dare daga wani, Kabiru Yusuf, da ke zaune kusa da gidan da ya rushe.

DUBA WANNAN: Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

"Ba muyi wata-wata ba wajen tura jami’an mu da kayan aikin ceto ciki harda mota, jami’an sun isa wajen da abun ya faru da misalin karfe 8:30 na daren."

Mutane biyu daga cikin wadanda aka ceto din sun rasu a kan hanyar kai su asibitin Malam Aminu Kano, sauran mutane hudun kuma suna nan rai a hannun Allah a asibitin.

Wadanda aka ceto din sune, Muhammad Malami, Abba Malami, Salim Malami, Asmau Malami, Maryam Malami, da Zainab Malami.

Har yanzu dai hukumomi suna binciken sanadin rushewar ginin, wanda ana kyautata zaton ruwan sama mai karfi da yake sauka ne ya jawo shi.

Ya kuma ce hukumar nazarin yanayi na kasa tayi hasashen cewa za'a samu ruwan sama fiye da yadda da shekarun baya saboda hakan ya shawarci mutanen da ke zaune a gidajen da ke da ramuka su toshe ramunkan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel