2019: Wata kungiya na son siyawa Buhari fam din takara a matsayi tukwicin dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas

2019: Wata kungiya na son siyawa Buhari fam din takara a matsayi tukwicin dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas

- Wata kungiya a yki arewa maso gabas na son ta siyawa Shugaba Buhari fam din takara

- A cewar kungiyar hakan tukwici ne ga Shugaban kasar saboda dawo da zaman lafiya da yayi a yankin arewa maso gabas

- Ta ce tana sane da sauran kungiyoyin da suka nemi siyan wannan fam din

Wata kungiyar wanzar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas mai suna North East Vanguard for Peace (NEVP), ta nuna ra’ayin son siyawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari fam din sake takara a matsayin tikwicin dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

Kungiyar yayinda tayi alkawarin jagorantar kudirin tazarcen Shugaba Buhari sunce duk da sun samu labarin cewa wasu kungiyoyi sun dauki alkawarin siyan wannan fam din, sai dai sunce saboda yaki a ta’addancin da Buhari yayi da kuma dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas, shugaban kasar ya cancanci fam din takara daga arwa maso gabas wadanda suka amfana daga mulkinsa.

2019: Wata kungiya na son siyawa Buhari fam din takara a matsayi tukwicin dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas

2019: Wata kungiya na son siyawa Buhari fam din takara a matsayi tukwicin dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas
Source: Depositphotos

Shugaban kungiyar na kasa, Dogo Danlami, a watasanarwa ga manema labarai yace wannan karamci nuni ne ga cewa mambobin kungiyar sun dauki ragamar jagorantar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin abu ne da cancanci suyi saboda ta’addancin Boko Haram ya shafe su sosai.

KU KARANTA KUMA: Kanin Dankwambo da na hannun damansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanki fam din nuna ra’ayin tsayawa takaran kujerar shuaban kasa a zabe mai zuwa karkashin jam’iyyarsa All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Kungiyar magoya bayan shugaban kasar mai suna Nigerian Consolidation Ambassadors Network ce ta siya fam din a madadin shugaban kasar a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

An dai siya masa fam din ne akan farashin da uwar jam’iyya ta nuna ra’ayin siyar da fam din dan takara wato naira miliyan 45.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel