Takarar Atiku: An yi harbin bindiga domin kwantar da rikici a ofishin PDP

Takarar Atiku: An yi harbin bindiga domin kwantar da rikici a ofishin PDP

An samu barkewar rikici da tashin tarzoma a hedkwatan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na kasa yayin da Atiku ya mayar da fam dinsa na takarar shugaban kasa a yau, Alhamis 6 ga watan Satumba 2018.

'Yan sanda na can yanzu haka suna harbe-harbe domin kwantar da tarzomar da ta tashi a shelkwatar ta PDP dake Abuja.

Rahoto daga jaridar Sahara Reporters ya bayyana cewa ihun 'Sai Baba' ya tada tarzoman da ya faru a shelkwatar jam'iyyar PDP a yau alhamis, 6 ga watan Satumba yayinda dan takaran shugaban kasa, Atiku Abubakar ya je mayar da takardan takara.

Yayinda matasa suka fara ihun 'Sai Baba', sai magoya bayan Atiku suka fusata da wannan abu suka fara fada tsakaninsu. Wannan abu yayi tsamari har ya bukaci jami'an yan sanda su harba bindiga domin kwantar da tarzoman.

KU KARANTA: An damke matasa 41 da ake zargi luwadi a taron banbadewa a jihar Bauchi

Zuwa yanzu, bamu samu rahoton cewa an samu rashin rayuka ko jikkatan wasu ba.

Irin wannan abu ya faru da wani dan takaran kujeran shugaban kasa kuma Sanata a yauzu, Rabi'u Musa Kwankwaso, a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja. Sannan aka sake masa ihun 'Sai Baba' a Masallacin Juma'a a jihar Kaduna.

Wannan abu kamar cewa masu sharhi na nuna cewa kada shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 zai yi wuya saboda wadanda ake ganin zasu iya kadashi ake ciwa mutunci a taro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel