An cafke wasu Soji da aka sallama dumu-dumu cikin aikata miyagun laifi

An cafke wasu Soji da aka sallama dumu-dumu cikin aikata miyagun laifi

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, an cafke wasu soji biyu da suka shahara da aikata miyagun laifi na safara da fataucin haramtattun hajoji a kasar nan a matsayin hanyar su ta yaki da zaman kashe wando.

Hukumar 'yan sandan ta Najeriya ta cafke wannan miyagu yayin da suke rakiyar wata babbar mota dauke da haja ta zunzurutun dukiya da ta kai kimanin N13.5m a can jihar Legas.

Sojin biyu sun amsa laifinsu nan take da cewar sun riki wannan mummunar sana'a tun yayin da aka sallame su daga bakin aiki a shekarar 2015 da ta gabata a matsayin hanyar su ta cin abinci da kaurace zaman banza.

Legit.ng ta fahimci cewa, sojin su na amfani da kakakin su na soji wajen aikata wannan tuggu a matsayin wata basaja ga gama garin al'umma.

An cafke wasu Soji da aka sallama dumu-dumu cikin aikata miyagun laifi

An cafke wasu Soji da aka sallama dumu-dumu cikin aikata miyagun laifi
Source: Depositphotos

Hukumar 'yan sandan jihar ta Legas da sanadin kakakin ta, Imohimi Edgal ya bayyana cewa, korarrun sojin sun shahara wajen yiwa matafiya fashi da makami sanye cikin kakakin su da suke yaudara wajen kwace da karkatar da motoci yayin da suka dauko dukiyar al'umma.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Kasa ta sheke 'yan ta'adda, ta ceto Dabbobi 147 da aka sace a jihar Borno

Hukumar sojin ta bayar da sunayen wannan miyagu da suka hadar da; Moses Johnson, tsohon ma'aikacin sojin kasa da kuma Akintola Abiodun, tsohon ma'aikacin sojin sama.

Johnson a yayin ganawarsa da manema labarai cikin shelkwatar 'yan sanda dake birnin Ikeja a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa, sun dauki wannan mummuna salo a matsayin hanyar cin abinci da kauracewa zaman banza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel