Yanzu Yanzu: Atiku da magoya bayansa sun mamaye hedkwatar PDP

Yanzu Yanzu: Atiku da magoya bayansa sun mamaye hedkwatar PDP

- Magoya bayan Atiku Abubakar sun mamaye manyan unguwanni zuwa Wadata Plaza, hedkwatar jam’iyyar dake Abuja

- Atiku zai gabatar da fam dinsa da ya yanka na takarar shugaban kasa a zaben 2019

- Tsohon mataimakin shugab an kasar dai ya nuna aniyarsa na takaran shugaban kasa

Magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujerar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar sun mamaye manyan unguwanni zuwa Wadata Plaza, hedkwatar jam’iyyar dake Abuja.

Magoya bayan nasa dake sanye da riga da hula mai dauke da rubutun “Atiku 2019” sun hana masu mota zarya yadda ya kamata, yayinda suke buga ganga da wakokin yabo ga mutumin da ake sa ran zai mayar da fam dinsa na takarar zaben shugaban kasa a 2019.

Matasa na dauke da kwalayen sanarwa da motocin da akayiwa kawa yayinda masu siyar da jaridu ke ta ciniki.

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Buhari suna bala'in tsoron ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP na zaben 2019 mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Ku yanki fam dinku a Abuja – APC ga yan takara

Haka zalika fitaccen dan siyasar ya kuma ce yana kalubalantar jam'iyyar ya zuwa wata muhawarar keke-da-keke akan abubuwan da suka shafi kasar da al'ummar cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel