Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi da filin jirgin saman Beijing ya nufo gida

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi da filin jirgin saman Beijing ya nufo gida

Jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Eagle 001, ya tashi daga babban filin jirgin saman birnin Beijing domin dawowa gida bayan halartan taro hadin kan kasar Sin da kasashen nahiyar Afirka FOCAC.

Shugaba Buhari ya tafi kasar Sin ranan Juma'a, 31 ga watan Agusta 2018 bayan karban bakuncin shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, a fadar shugaban kasa, Aso Villa.

An gudanar da wannan taro ne karo na bakwai a wannan mako a kasar Sin inda shugabannin kasashen Afrika daban-daban suka halarta.

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a wannan taro inda ya bayyana alfanun da Najeriya ta samu a hadin kan da take yi da kasar Sin. Kana ya karyata rahotannin cewa Najeriya ba tada kudin biyan basussukan da take karba daga hannun gwamnatin kasar.

KU KARANTA: Kamfanin Ruyi za su sanya hannun jarin $200m a Kano, Katsina, Legas da Abia bayan ganawarsu da Buhari a Sin

Daga cikin tsarabar da Buhari dawo da su, akwai alkawarin gina masana'antu, layin dogo, da sanya hannun jari a jihohi daban-daban.

A jiya Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin kamfanin ‘Ruyi Group, wata babbar kamfanin a kasar Sin inda suka tattauna kan irin hannun jarin da za su sanya a Najeriya.

Bayan ganawar, kamfanin ta alanta cewa za ta sanya hannun jarin dala miliyan dari biyu ($200m) wajen gina tashar mota a jihar Kano, gonan auduga a jihar Katsina, da masaka a jihar Abiya da Legas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel