Boko Haram yan tawayen Musulunci bane – Sheik Ahmad

Boko Haram yan tawayen Musulunci bane – Sheik Ahmad

- Babban farfesa, Ahmad Okene, ya nisanta Boko Haram da addinin Musulunci

- Ya gabatar da lakca kan tarihin Boko Haram tun shekarar 2009

Wani shahrarren malami addini, Farfesa Ahmad Okene Ahmad, ya bayyana cewa ya kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Liddaawati Wal-jihad, da aka fi sani da Boko Haram basuda alaka da koyarwan addinin Musulunci.

Babban malamin wanda yayi jawabi a taron lakcan babbar jami’ar Soji wato NDA a ranan Talata, 4 ga watan Satumba a jihar Kaduna, ya ce yan Boko Haram sun hallaka akalla shahrarrun malaman addini 200 tsakanin shekarar 2011 da 2015.

KU KARANTA: Kamfanin Ruyi za su sanya hannun jarin $200m a Kano, Katsina, Legas da Abia bayan ganawarsu da Buhari a Sin

Lakcan mai take: “Boko Haram tun 2009: Nazari cikin tarihin tsaro,” ya ce: “ Ko shakka babu ana iya alakanta Boko Haram da Musulunci amma a matsayin yan tawaye.”

“Shugabannin Boko Haram sun dade suna kokarin halalta ayyukan da sukeyi ta hanyar amfani da ayoyin Al-Kur’ani da hadisai wanda suka fahimta a jahilce.”

Game da cewarsa, daga cikin ayyukan da sukeyi shine garkuwa da yan mata da kuma tilastasu karbar addinin Musulunci yayinda addinin ya koyar da cewa babu tilastawa a cikin Islama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel