Ku yanki fam dinku a Abuja – APC ga yan takara

Ku yanki fam dinku a Abuja – APC ga yan takara

- Jam'iyyar APC bukaci yan takaranta dake neman kujerun majalisar dokoki na jiha, wadanda basu siya takardan takaransu ba a jihohinsu da su zo sakatariyar jam’iyyar

- Hakan ya byo ban korafe-korafe da ta samu na cewa an kimallaka masu fam din a jihohinsu

A watan Satumban nan ne dai za'a gudana da zabukn fidda gwani

Jam’iyyar All Progressives Congress ta bukaci yan takaranta dake neman kujerun majalisar dokoki na jiha, wadanda basu siya takardan takaransu ba a jihohinsu da su zo sakatariyar jam’iyyar.

Jam’iyyar a wata sanarwa da ta fitar ta mukaddashin sakaaren labaranta na kasa, Yekini Nabena, yace jam’iyyar ta samu korafi daga wasu yan tara kujerun majalisar jiha cewa basu samu damar mallakar fam din ba.

Ku yanki fam dinku a Abuja – APC ga yan takara

Ku yanki fam dinku a Abuja – APC ga yan takara
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa: “a daidai lokacin da aka fara siyar da fam din takara domin zabukan 2019, mun samu korafe-korafe daga wasu yan takaran majalisar dokoki na jiha kan rashin samun damar mallakar fam din raayin takara a jihohinsu.

“Yan takaran da abun ya shafa na iya zuwa sakatariyar PDP na kasa dake Abuja domin mallakar fam bayan sun biya kudaden da yakamata a bankunan da aka bukata.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar soji sun kashe yan ta’adda, sun samo dabbobi 147 da aka sace a Borno

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan ta tace za’a samar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct”kenan a turance.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel