Hukumar Sojin Kasa ta sheke 'yan ta'adda, ta ceto Dabbobi 147 da aka sace a jihar Borno

Hukumar Sojin Kasa ta sheke 'yan ta'adda, ta ceto Dabbobi 147 da aka sace a jihar Borno

A ranar yau ta Alhamis hukumar sojin kasa ta Najeriya ta bayyana cewa, ta samu nasarar sheke wasu 'yan ta'adda na Boko Haram yayin wani simame da ta kai kauyukan Jentilo da Gesada na kananan hukumomin Kukawa da kuma Guzamala dake jihar Borno.

Bayan ga wannan nasara hukumar sojin a yayin simamen ta ceto kimanin dabbobin kiwo 147 da 'yan ta'addan suka sace na al'ummar jihar ta Borno.

Kakakin hukumar Sojin na kasa, Birgediya Janar Texas Chukwu, shine ya bayyana cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Maiduguri.

Hukumar Sojin Kasa ta sheke 'yan ta'adda, ta ceto Dabbobi 147 da aka sace a jihar Borno

Hukumar Sojin Kasa ta sheke 'yan ta'adda, ta ceto Dabbobi 147 da aka sace a jihar Borno
Source: Facebook

Birgediya Chukwu yake cewa, dakarun Operation Lafiya Dole tare da hadin gwiwar kungiyar dakaru ta 'yan sa kai, ke da alhakin gudanar da wannan gagarumar bajinta ta batar da 'yan ta'addan da suka shahara akan yiwa al'umma sace-sacen kudi da dabbobi a kauyukan.

KARANTA KUMA: Gwamna Ortom ya sallami Hadimansa 28 a jihar Benuwe

A yayin ci gaba da ganawar sa da manema labarai, Chukwu ya kuma bayyana cewa dakarun sojin sun samu nasarar kwato muggan makamai da suka hadar da bindigu kirar AK47.

Legit.ng kamar yadda kakakin hukumar sojin ya bayyana ta fahimci cewa, an maidawa da mamallakan wannan dabbobi dukiyarsa bayan an gudanar da bincike na tantancewa bisa ga jagoranci na dagaci da kuma shugaban dakaru na sa kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel