Ni kadai ne APC da Buhari ke tsoron in samu tikitin takarar shugaban kasa na PDP - Saraki

Ni kadai ne APC da Buhari ke tsoron in samu tikitin takarar shugaban kasa na PDP - Saraki

- Saraki ya kalubalanci Buhari a muhawarar keke-da-keke

- Yace shi kadai ne APC da Buhari ke tsoron ya samu tikitin takarar PDP

Shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da Buhari suna bala'in tsoron ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP na zaben 2019 mai zuwa.

Ni kadai ne APC da Buhari ke tsoron in samu tikitin takarar shugaban kasa na PDP - Saraki

Ni kadai ne APC da Buhari ke tsoron in samu tikitin takarar shugaban kasa na PDP - Saraki
Source: Facebook

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta taso keyar wani Sanatan PDP a gaba

Haka zalika fitaccen dan siyasar ya kuma ce yana kalubalantar jam'iyyar ya zuwa wata muhawarar keke-da-keke akan abubuwan da suka shafi kasar da al'ummar cikin ta.

Legit.ng ta samu cewa dukan wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na gangamin yakin neman tikitin takarar na Dakta Saraki watau Yekini Nabeda ya fitar.

Idan mai karatu bai manta ba dai shugaban majalisar ta dattijai ya fice daga jam'iyyar APC ne inda ya koma jam'iyyar sa ta asali ta PDP sakamakon abun da ya kira rashin adalcin da ake yi masa.

A wani labarin kuma, Wasu matasa a karkashin inuwar kungiyar 'Zauren Olanrewaju Oba' dake a jihar Kwara, shiyyar Arewa ta tsakiya sun sha alwashin gudanar da gangamin matasa miliyan daya don nuna goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasar Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Shugaban matasan Olanrewaju Oba yace gangamin ya zama dole ne a gare su musamman ma duba da irin kyawawan kudurorin sa ga al'ummar Najeriya tun sadda yake gwamna a jihar ta Kwara da ma shugaban majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel