Zaben 2019: Matasa miliyan 1 a Arewa za su nuna goyon bayan su ga wani dan takarar Shugaban kasa

Zaben 2019: Matasa miliyan 1 a Arewa za su nuna goyon bayan su ga wani dan takarar Shugaban kasa

- Matasa miliyan 1 a Arewa za su nuna goyon bayan su ga Saraki

- Sunce tabbas ya taka rawar gani a dukkan mukaman da ya rike a baya

- Sun shawarci jam'iyyar PDP da ta ba shi tikitin takarar ta

Wasu matasa a karkashin inuwar kungiyar 'Zauren Olanrewaju Oba' dake a jihar Kwara, shiyyar Arewa ta tsakiya sun sha alwashin gudanar da gangamin matasa miliyan daya don nuna goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasar Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Zaben 2019: Matasa miliyan 1 a Arewa za su nuna goyon bayan su ga wani dan takarar Shugaban kasa

Zaben 2019: Matasa miliyan 1 a Arewa za su nuna goyon bayan su ga wani dan takarar Shugaban kasa
Source: Twitter

KU KARANTA: Ban taba satar ko da kwandala ba tun da nike - Atiku

Shugaban matasan Olanrewaju Oba yace gangamin ya zama dole ne a gare su musamman ma duba da irin kyawawan kudurorin sa ga al'ummar Najeriya tun sadda yake gwamna a jihar ta Kwara da ma shugaban majalisar dattawa.

Legit.ng ta samu cewa Mista Olanrewaju ya kuma kara da cewa ranar sha shida ga watan Satumbar da muke ciki ne suka sa domin gudanar da wannan gangamin kuma su na sa ran halartar matasa daga kowace bangare na Najeriya.

Daga nan ne kuma yayi anfani da damar wajen kira ga wadanda ke da alhakin yin zaben 'yan takara a jam'iyyar PDP watau deliget da su zabi gwanin nasa.

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da Buhari suna bala'in tsoron ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP na zaben 2019 mai zuwa.

Haka zalika fitaccen dan siyasar ya kuma ce yana kalubalantar jam'iyyar ya zuwa wata muhawarar keke-da-keke akan abubuwan da suka shafi kasar da al'ummar cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel