Rashawa: Hukumar EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

Rashawa: Hukumar EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

- Hukumar EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

- EFCC din na tuhumar sa da karbar rashawa na motocin Naira miliyan 254

- Yanzu dai shi kadai ne Sanatan PDP a jihar Akwa Ibom

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice ta shigar da kara a wata babbar kotu dake a garin Legas akan wani Sanata daga jihar Akwa Ibom game da almundahana ta wasu makudan kudade.

Rashawa: Hukumar EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

Rashawa: Hukumar EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Shugaba Buhari na shirin korar wasu kusoshin gwamnatin sa

Kamar yadda muka samu Sanatan mai suna Albert Bassey EFCC na tuhumar sa ne da laifin ansar cin hancin motoci 12 da kudin su ya kai Naira miliyan 254 daga hannun wani dan kasuwa a lokacin yana kwamishinan kudi a jihar ta Akwa Ibom.

Legit.ng ta samu cewa yanzu haka dai Sanata Albert Bassey shi kadai ne ya rage a jam'iyyar PDP a jihar biyo bayan ficewar sauran biyu da suka hada da Sanata Godswill Akpabio da kuma Nelson Effiong da suka koma APC a kwanan baya.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace shi tun da Allaha yayi shi bai taba satar ko da kwandala ba.

Fitaccen dan siyasar haka zalika ya kalubalanci duk wani mai shaidar cewa ya taba karkatar da dukiyar al'umma ko kuma wata rashawa ko cin hanci da ya fito ya fallasa hakan a idon duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel