Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC a jihar nan tayi fatali da tsarin kato-bayan-kato

Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC a jihar nan tayi fatali da tsarin kato-bayan-kato

- Jam'iyyar APC a jihar Ogun tayi fatali da tsarin kato-bayan-kato

- Tace tsarin kato-bayan-kato zai haifar da rikici

Jam'iyya ma mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) shiyyar jihar Ondo tayi fatali da tsarin zaben fitar da gwani na kato-bayan-kato a ranar Larabar da ta shude biyo bayan wani zama da jiga-jigan ta suka yi a garin Akure, babban birnin jihar.

Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC a jihar nan tayi fatali da tsarin kato-bayan-kato

Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC a jihar nan tayi fatali da tsarin kato-bayan-kato
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Fada ya kacame tsakanin Kwankwaso da Shekarau a Kano

Da yake yin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron na masu ruwa da tsakin jam'iyyar a jihar, Satana Tayo Alasoadura dake wakiltar mazabar shiyyar jihar ta tsakiya ya ce sun yanke shawarar ne bayan doguwar muhawara.

Legit.ng ta samu cewa Sanata Tayo Alasoadura ya cigaba da cewa dukkan masu ruwa da tsakin jam'iyyar a jihar daga karshe sun yi ittifakin cewa tsarin kato-bayan-kato zai jawo matsala babba idan aka yi shi.

Mai karatu da zai iya tuna cewa jam'iyyar ta APC a mataki na kasa ta zabi yin zabukan fitar da gwanin shugaban kasa ta hanyar tsarin kato-bayan-kato.

A wani labarin kuma, Batun takarar shugabancin kasa da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ke yi da alama za ta fuskanci babbar cikas a yayin ake ta rade-raden cewa daya daga cikin kannen sa, watau Buhari Mohammed Dankwambo da aka fi sani da BHD, ya kammala shirin fita daga PDP ya koma APC.

Da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Buhari Mohammed Dankwambo yace tuni ya gama yanke shawarar fita daga PDP zuwa APC din kuma yana jiran umurnin uwar jam'iyya ne kawai da zata saka ranar karbar sa da dumbin magoya bayan sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel