Yaki da cin hanci da rashawa: An fatattaki mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya

Yaki da cin hanci da rashawa: An fatattaki mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta yunkura ta sallami mataimakin mai horas da yan kwallon kwallon kafa ta Najeriya, Salisu Yusuf na tsawon shekara daya biyo bayan kamashi da tayi da laifin amsan cin hanci, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito NFF ta dauki wannan mataki ne bayan wani bidiyo ya bayyana inda aka nuna lokacin da Salisu ya karbi wasu makudan kudade da suka kai dala dubu daya daga hannun wani dan jarida da yayi basaja a matsayin wakilin wasu yan kwallon Najeriya.

KU KARANTA: Y’aƴan kungiyar matsafa sun yanke kan wani dansandan MOPOL a Jos

Haka zalika NFF ta bukaci Salisu daya biya taran kudi dala dubu biyar cikin watanni uku, kamar yadda kwamitin binciken data kafa a karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya bukata.

Yaki da cin hanci da rashawa: An fatattaki mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya
Caoch Salisu
Asali: Depositphotos

Rahoton kwamitin yace: “Mun tabbatar da Salisu ya karbi cin hancin dala dubu daya daga wakilin dan kwallo Osas Okoro da Rabiu Ali domin a sanyasu cikin gasar kwallon kafa ta CHAN 2018, kamar yadda ya amsa da kuma yadda muka gani a bidiyon.

“Kwamitin ya gano da gangan Salisu ya amshi wannan kudi, daga mutanen nan da suka bashi cin hanci don ya sanya yan wasannan a gasar, sai dai bamu samu wani shaida dake nuna cewa tabbas Salisu ya sanya ne saboda wannan kudi ba,

“Amma abinda Salisu yayi ya bata sunan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, kuma yayi karan tsaye ga yarjejeniyar daya rattafa hannu akai tsakaninsa a da hukumar NFF a lokacin da ta bashi aiki,

"kamata yayi ayyukansa na fili da na boye su zama abin koyi, don haka ya zama wajibi a hukunta shi duk da cewa wannan ne karo na farko da aka kama shi da laifi, amma ba komai ya zama izina ga sauran jama’a.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel