Talauci ne babbar matsalar kasar nan ba komai ba – Kwankwaso

Talauci ne babbar matsalar kasar nan ba komai ba – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa talauci ne babbar matsalar kasar nan kuma a dalilin sakacin Gwamnatin Tarayya ne ake fama da wannan musiba har gobe.

Talauci ne babbar matsalar kasar nan ba komai ba – Kwankwaso

Kwankwaso yace duk lalacewar PDP ta fi Jam’iyyar APC
Source: Depositphotos

Injiniya Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara Jihar Abiya inda ya gana da Mai girma Gwamnan Jihar watau Ifeanyi Ikpeazu a Umuahia. ‘Dan takarar Shugaban kasar yace APC ba ta rike kasar nan yadda ya kamata ba cikin shekaru 3.

Channels TV ta rahoto Kwankwaso yana cewa a tunanin su PDP ta ba mutane kunya, sai kuma su ka ga ashe duk lalacewar Jam’iyyar, ta fi APC. Tsohon Gwamnan yace APC ba tayi amfani da damar da ta samu a kan Gwamnati ba.

KU KARANTA: Kwankwaso ya maida fam da tsayawa takarar Shugaban kasa a PDP

Sanata Kwankwaso yake cewa da su aka yi wa APC hidimar karbe mulki daga hannun PDP amma kuma sun gane shayi ruwa ne. Babban ‘Dan siyasar yace shugabancin APC ta gaza maganin rashin aikin yi da matsalar tsaro a kasar nan.

A jawabin ‘Dan takarar shugaban kasar, ya bayyana cewa talauci ne ya fi damun Najeriya ba komai ba. Tsohon Gwamnan yake cewa dole shugabanni su rika magance barnar da ake yi a Gwamnatin domin fitar da jama’a daga wahala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel