Gungun yan bindiga sun bindige masu hakar ma’adanai 11 a Filato

Gungun yan bindiga sun bindige masu hakar ma’adanai 11 a Filato

Wasu gungun yan bindiga da har yanzu ba’a san ko su wanene ba sun kai ma wasu mutane dake hakat ma’adanan kasa jari a jihar Filato, inda suka halaka mutane da dama, inji rahoton jaridar premium times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Talata 4 ga watan Satumba kamar yadda rundunar Yansandan jahar ta bayyana a cikn sanarwar data fitar ma manema labaru a Laraba, 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta biya masa naira miliyan 45 kudin takara

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Terna Tyopev ya bayyana cewa yan bindigan sun kai wannan hari ne a wani wurin hakar ma’adanan kasa dake kauyen Gana-Ropp cikin karamar hukumar Barikin Ladi, inda suka kashe mutane goma sha daya.

“A ranar Talata da misalin karfe 12:30 na rana ne dakacin kauyen Gana-ropp, Da Gyan Pam ya kiramu a waya yana shaida mana cewa sun ji karar harbe harbe a wani yankin da ake hakar ma’adanan kasa.

“Ba tare da wata wata ba muka aika da tawagar Yansandanmu, a karkashin Dansanda mai mukamin DPO, da isarsu sai suka tarar da mutane goma sha daya kwance cikin jini, da suka bincika sai suka gane biyar daga cikinsu sun mutu.

“Nan take suka garzaya da sauran mutane shida da suka samu munanan rauni zuwa asibiti, amma fa basu wani jima a Asibitinba suka ce ga garinku nan, kamar yadda likitocin Asibitin suka tabbatar, kuma tuni aka mika gawarwakinsu ga iyalansu.” Inji Terner.

Sai dai kaakakin yace koda tawagar yansandan ta isa inda lamarin ya faru, basu iske yan bindigan ba, amma a yanzu haka sun kaddamar da bincike don gano masu hannu cikin wannan ta’asa. Don haka ya nemi jama’a dasu taimaka musu da bayanan da zasu taimaka musu a aikinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel