PDP ta shawo kan ‘Ya ‘yan ta domin doke APC a zaben Osun

PDP ta shawo kan ‘Ya ‘yan ta domin doke APC a zaben Osun

Mun ji cewa PDP ta samu hada-kan manyan ‘Yan siyasar da su kayi takarar fitar da gwani na Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai Ademola Adeleke da Akin Ogunbiyi sun amince su yi aiki tare.

PDP ta shawo kan ‘Ya ‘yan ta domin doke APC a zaben Osun

Bukola Saraki ya sulhunta Sanata Adeleke da Akin Ogunbiyi
Source: Twitter

‘Dan takara Ademola Adeleke da kuma abokin hamayyar sa Dr. Akin Ogunbiyi sun ajiye banbancin su domin doke a Jam’iyyar APC a zaben da za ayi a karshen watan nan a Osun. Bukola Saraki ne dai yayi kokarin sulhunta ‘yan siyasar.

Idan ba ku manta ba Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne aka daurawa alhakin kawowa Jam’iyyar PDP nasara a zaben Gwamna da za ayi a Jihar Osun. Yanzu dai Saraki ya fara aikin da ake so inda ya dinke barakar PDP ta cikin-gida.

KU KARANYA: Dankwambo zai rasa wasu na-kusa da shi a PDP

Shugaban Majalisar kasar ya bayyana cewa an samu jituwa tsakanin manyan masu neman Gwamna a Osun inda kowane cikin su ya sa hannu a wata yarjejeniya da aka shiga. Adeleke da Ogunbiyi sun yi alkawarin hada-aki a zaben Jihar.

Wasu Jaridun ma sun rahoto cewa duka manyan PDP sun yi alkawarin cewa za su yi wa Jam’iyyar aiki ne a zaben Gwamna da za ayi a Jihar Osun a karshen wannan watan. Manyan ‘Yan siyasar sun ji dadin wannan abu da Saraki yayi daf da zaben.

Sanata Ademola Adeleke ne ya lashe zaben fitar da gwani na PDP da aka yi wanda ya jawo bangaren Dr. Ogunbiyi su kace ba za su yarda ba. Yanzu dai ‘Yan siyasar sun fahimci juna kuma sun sha alwashin tika Jam’iyyar APC da kasa a Jihar kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel