Kwankwaso ya cike fam din tsayawa takaran 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP

Kwankwaso ya cike fam din tsayawa takaran 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP

Daya daga cikin manyan ‘Yan takarar Shugaban kasa a karkashin PDP Sanata Rabiu Musa Kwanwakaso ya shirya fafatawa a zabe mai zuwa inda har ya cika fam din da ya karba ya maidawa Jam’iyya.

Kwankwaso ya cike fam din tsayawa takaran 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP

Rabiu Musa Kwankwaso bayan ya mika fam din sa na takaran 2019

Kamar yadda mu ka samu labari daga shafin ‘Dan takarar na Shugaban kasa Kwankwaso, tuni dai har ya cika fam din sa na tsayawa a zaben 2019 ya maidawa Hedikwatar Jam’iyyar PDP na kasa kamar yadda doka ta tanada.

Tsohon Gwamnan na Kano ya daura damarar shiga zabe da sauran ‘Yan takarar Shugaban kasa a PDP irin su Atiku Abubakar, Sule Lamido, Bukola Saraki da sauran su. Za a fitar da ‘Dan takarar PDP ne dai kwanan nan.

Bayan Kwankwaso ya mika fam din na sa a ofishin Sakataren gudunarwa na Jam’iyyar PDP watau Kanal Austin Akobundu mai ritaya, ya kuma kai wa Shugaban PDP na kasa watau Prince Uche Secondus ziyara a ofishin sa.

KU KARANTA: Buhari na fuskantar wani matsin lamba a Gwamnati

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa gaba daya Uche Secondus ya taya Sanata Rabiu Kwankwaso addu’ar samun sa’a a zaben mai gabata. Manyan wadanda ke tare da Kwankwaso irin su Buba Galadima su na cikin tawagar.

Jiya kun ji cewa babban Jakadan Kasar Ingila a Najeriya Paul Arkwright ya kai wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ziyara a gidan sa da ke Maitama a cikin babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja inda su kayi wata tattaunawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel