Gwamna Ortom ya sallami Hadimansa 28 a jihar Benuwe

Gwamna Ortom ya sallami Hadimansa 28 a jihar Benuwe

Zaku ji cewa tsananin adawa dake tattare cikin siyasa musamman ta kasar nan ta sanya gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya fatattaki hadiman gwamnatin sa kimanin 28 kamar yadda rahotanni da sanadin shafin jaridar The Nation suka bayyana.

Rahotannin sun bayyana cewa, gwamnan ya sallami hadiman sa na musamman guda 17, yayin ya yiwa manyan hadiman sa 11 sallama ta 'Umma ta gaida Assha' cikin ruwan sanyi domin yiwa gwamnatin sa garambawul da sauya fasalin 'yan majalisa da makarrabansa.

Sakataren gwamnatin jihar, Tony Ijoho, shine ya bayar da sanarwa yanke alakar hadiman 28 da kuma gwamnan jihar, inda ya neme su akan mika dukkanin wani mallaki na gwamnatin a hannun sakatarorin su na dindindin.

Gwamna Ortom ya sallami Hadimansa 28 a jihar Benuwe

Gwamna Ortom ya sallami Hadimansa 28 a jihar Benuwe
Source: Depositphotos

Binciken manema labarai ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta raba gari da hadimanta ne domin bai wa sabbi dama ta maye guraben su musamman 'yan jam'iyyar adawa ta PDP.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan Mutane 9 da jikkatar 5 a jihar Kano

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Ortom ya karbi ragamar gudanar da al'ummar jam'iyyar PDP tun yayin da ya sauya sheka ta ficewa daga jam'iyyar APC.

Gwamnan yana daya daga cikin jiga-jigan kasar nan da guguwar sauyin sheka ta kada su yayin da suka yi hannun riga da jam'iyyar ta APC makonni kadan da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel