An gano ashe yan ta'adda sun kutsa cikin jama'a a sansanonin gudun hijira

An gano ashe yan ta'adda sun kutsa cikin jama'a a sansanonin gudun hijira

- Akwai yan leken asiri daga ISIS a sansanin gudun hijirar jihar Borno

- Sune ke tada hankula ba tare da an gano su ba a sansanin

- Mutane su bada hadin kai don tsamo su

An gano ashe yan ta'adda sun kutsa cikin jama'a a sansanonin gudun hijira

An gano ashe yan ta'adda sun kutsa cikin jama'a a sansanonin gudun hijira
Source: Twitter

Hukumar yan sandan jihar Borno tace akwai wani sashen yan leken asirin ISIS dake cikin sansanin gudun hijirar jihar Borno.

Mataimakin kwamishinan yan sandan jihar, Ahmed Bello ya bayyana hakan a lokacin da yake bada bayanin tsaro a zauren Humanitarian and Development Coordination a Maiduguri.

Mun samu rahoton cewa, Bello ya wakilci kwamishinan yan sandan jihar ne, Demien Chukwu, yace uku daga cikin yan ta'addan Boko Haram da aka kama wata biyu da suka gabata, yan ISIS ne.

Ya bayyana yanda yan ta'addan ke tada husuma a sansanin ba tare da an gano su ba.

DUBA WANNAN: Tallafi ga ilimin Boko a jihar Kano

Su dai ISIL sun dage sai sun mulki yankunan kasashe wadanda ke da musulmai a ciki, kuma wani bangare na Boko Haram sun yi mubayi'a ga kungiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel