Ambaliyar ruwa ya hallaka mutane da dama a jihar Niger

Ambaliyar ruwa ya hallaka mutane da dama a jihar Niger

Wata uwa mai goyo da danta tare da wasu mutane sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a karamar hukumar Kontogora dake jihar Niger a ranar Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa na jiha (NSEMA) ya tabbatar a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

An tattaro cewa matar Bafulatana ce goye da danta a bayanta, darakta janar na NSEMA, Malam Ahmed Ibrahim Inga ya fadi.

“Bazamu iya sanin ko wacece ba da kuma inda ta fito saboda babu wani da ya santa,” inji Malam Inga.

Ambaliyar ruwa ya hallaka mutane da dama a jihar Niger

Ambaliyar ruwa ya hallaka mutane da dama a jihar Niger
Source: Twitter

Yace daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai yarinya yar shekara hudu, Ummi Khaira wacce ta rasa ranta bayan ginin laka ya rufto mata a inda ta fake tare da sauran yara yankin Rigara.

Haka zalika an tabbatar da mutuwar wani matashi wadda ya rubuta jarrabawar shiga jami’a kwanaki biyu kafin nan.

KU KARANTA KUMA: 2019: Tawagar yakin neman zaben Saraki sun isa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas

An tattaro cewa yana buga kwallon kafa tare da sauran matasa lokacin da yake neman mafaka.

An kuma tsinci gawar wani mutumi mai shekaru 47 Umar Gaya na unguwar Gwari a ranar Talata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel