Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da magoya bayan Shugaba Buhari

Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da magoya bayan Shugaba Buhari

- Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da magoya bayan Shugaba Buhari

- Yace sam mulkin Shugaba Buhari yayi hannun riga da demokradiyya

- Yace Shugaban kasar bai cancanci tazarce ba

Daya daga cikin manyan malaman addinan kirista a kasar nan kuma shugaban rukunin majami'un Mount Zion Faith Global Liberation Ministry Inc.( a.k.a. By Fire By Fire) da ke a garin Nnewi, jihar Anambra mai suna Bishop Abraham Udeh ya yi kaca-kaca da masoya Muhammadu Buhari.

Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da magoya bayan Shugaba Buhari

Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da magoya bayan Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Atiku ya zayyana wasu matsalolin Buhari

Bishop din wanda a jiya ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa dukkan masu son Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zarce to lallai shi babban makiyin demokradiyya ne.

Legit.ng ta samu cewa ya kuma kara da cewa kusan dukkan shika-shikai da sharuddan demkradiyya shugaban kasar da gwamnatin sa sun sa kafa sun shure su a lokuta da dama a lokacin mulkin su.

Haka zalika babban bishop din ya bayar da misali da yadda bangaren zartarwa ya rika yiwa bangaren majalisar shigar hanci da kudundune tare da kasalandan lamarin da ya ce sam bai dace ba.

A wani labarin kuma, Akalla manyan malaman addinin kirista da suka kai matsayin bishof-bishof su saba'in da biyar aka sa ran za su taru a garin Sokoto mai dumbin tarihi kuma daular musulunci dake a shiyyar Arewa ta yamma daga Shidda ga watan Satumba domin gabatar da wani gagarumin taron karawa juna sani.

Daya daga cikin mahalarta taron kuma mai masaukin baki Bishop Matthew Kukah dake zaman shugaban malaman addinin kiristan na kabilar katolika shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel