Kai sumame gidan Edwin Clark: Ya zama wajibi a tsige Sifeta Janar na yan sanda - Timi Frank

Kai sumame gidan Edwin Clark: Ya zama wajibi a tsige Sifeta Janar na yan sanda - Timi Frank

- Kwamred Timi Frank, ya yi kira da babbar murya da a sauke Sifeta Janar na yan sanda, Ibrahim Idris daga mukaminsa

- Frank ya ce sumamen da wasu jami'an yan sanda suka kai gidan Chief Clark ya nuna rashin kwarewar jagorancin rundunar da IGP Idris ya nuna

- Kwamred Frank, ya yi kira ga dukkanin al'umar Ijaw da su adana katin zabensu don tsige gwamnati mai ci a yanzu a zabe na 2019

Tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC, Kwamred Timi Frank, ya yi kira da babbar murya da a tsige Sifeta Janar na yan sanda, Ibrahim Kpotum Idris, bisa dalilin kai sumame gidan kwamishinan watsa labarai na kasa, kuma shugaban yankin Ijaw, Chief EdwinClark, da wasu jami'an yan sanda suka yi ba bisa ka'ida ba.

Frank ya ce wannan kai sumame ba bisa ka'ida ba, ya nunawa duniya cewa bai da siffofin shugabancin rundunar, uwa uba maras darajta kundin tsarin kasa da dokar tafiyar da tsarin rundunar ta kasa, inda ya kara da cewa "Yan Nigeria sun gaji gaji da irin wannan sakaci da nuna rashin kwarewa da Sifeta Janar ya ke nunawa."

Idan za'a iya tunawa, Legit.ng ta ruwaito maku cewa, a ranar talata jami'an rundunar yan sanda ta kai sumame gidan Chief Clark na Abuja, don bincike akan zargin an ajiye makamai a gidan, sai dai daga baya, mai magana da yawun rundunar, Jimoh Moshood a cikin wata sanarwa ya roki afuwa tare da nesantar da Sifeta Janar na rundunar daga kai sumamen.

KARANTA WANNAN: 2019: Ba zanyiwa IGBO shamaki da fadar shugaban kasa ba - Bafarawa

Kai sumame gidan Edwin Clark: Ya zama wajibi a tsige Sifeta Janar na yan sanda - Timi Frank

Kai sumame gidan Edwin Clark: Ya zama wajibi a tsige Sifeta Janar na yan sanda - Timi Frank
Source: Twitter

Da ya ke maida martani akan wannan sanarwa a ranar laraba a Abuja, Kwamred Frank, ya ce duk da cewa rundunar ta bayar da hakuri, wannan aika aikar ta nuna cewa Sifeta Janar na rundunar bashi da kwarewar shugabancin rundunar.

Da ya ke Allah wadai da wannan sumame da rundunar yan sanda ta kai gidan Chief Clark, tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na APC, ya buga misali da irin sumame da rufe majalisar dokoki ta kasa da rundunar tsaro ta fararen kaya DSS tayi, wanda ya zama silar korar shugaban hukumar, Lawal Daura.

"Wannan kai sumamen gidan Pa Clark abin ayi kwakkwaran bincike ne kana a gurfanar da dukkanin wadanda ke da hannuna ciki don fuskantar hukunci, in ba haka ba kuwa, zamu yanke hukuncin cewa ana kokarin kulla tuggun kashe Chief Clark, don haka dole ne a sauke Sifeta Janar na rundunar indai ana so ayiwa Clark adalci," a cewar Frank.

Kwamred Frank, ya yi kira ga dukkanin al'umar Ijaw da su adana katin zabensu don tsige wannan gwamnati mai ci a yanzu a zabe na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel