Canja sheka ba zai bawa masu cin hanci mafaka ba - Magu

Canja sheka ba zai bawa masu cin hanci mafaka ba - Magu

- Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya ce sauya jam'iyya ba zai bawa 'yan siyasa da ake tuhuma kariya ba

- Magu ya kuma ce babu wanda ya taba bashi umurnin dakatar da wani bincike da ya fara

- Shugaban hukumar ya yi kira da 'yan jarida su taimaka wajen wayar da kan jama'a

Ibrahim Magu, Shugaban riko na hukumar yaki da rashawa da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya ce canja sheka da 'yan siyasa ke yi ba zai hana hukumar ta cigaba da gudanar da binciken ta a kan yan siyasan ba.

Cikin yan kwanakin nan, wasu na zargin cewa dukkan 'yan siyasan da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressive Congress APC, sun tsira daga hukumar EFCC.

Canja sheka ba zai bawa masu cin hanci mafaka ba - Magu

Canja sheka ba zai bawa masu cin hanci mafaka ba - Magu
Source: Depositphotos

Amma a hirar da ya yi da 'yan jarida a Legas yau Laraba, Magu ya ce babu inda 'yan siyasa da suka sace kudin jama'a za su koma da zai hana hukumar bincikarsu.

DUBA WANNAN: Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

"Kawai don dan siyasa ya sauya sheka daga wata jam'iyya zuwa wata ba zai hana mu dakatar da binciken da muke akansa ba. Bamu dena bincike sai mun kammala.

"Kotu ne kadai ke da ikon wanke mutane daga zargi muddin an gurfanar dashi a gabanta," inji Magu.

A yayin da yake mayar da martani kan zargin da ake na cewa jam'iyyar APC tana yi masa katsalandan cikin aikinsa, Magu ya ce babu wanda ya taba bashi umurnin ya dakatar da binciken da ya keyi.

"Tun farko ni ba irin mutumin da za'a bashi umurnin ya dakatar da bincike ban," inji shi.

Shugaban na EFCC ya ce yanzu duk wani wanda ake bincike yana fakewa da siyasa ne musamman yanzu da babban zaben 2019 ke karatowa.

Ya kara da cewa kafafen yada labarai suna da muhimmiyar ruwa da zasu taka wajen wayar da kan jama'a saboda baragurbin 'yan siyasa da barayin dukiyar jama'a su dena amfani da siyasa don rudar jama'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel