Wani gwani a Kudu ya tsine wa duk mai sauya jam'iyya zuwa APC

Wani gwani a Kudu ya tsine wa duk mai sauya jam'iyya zuwa APC

- Wani basarake kuma jigo a jam'iyyar APC, Osemede Adun, ya sauya sheka daga zuwa PDP

- Ya tsinewa duk wanda ya fice daga PDP ya koma APC

- Cif Adun ya ce tsabar rashin adalci ta sa ya fice daga APC

Wani babban basarake kuma Ciyaman din sabuwa jam'iyyar APC (R-APC), Cif Osamede Adun ya tsinewa dukkan wanda ya shigo jam'iyyar PDP kuma daga baya ya koma jam'iyyar APC.

Kamar yadda Trubune ta ruwaito, Ayabahan na Benin ya jagoranci dubban 'yan Kwankwasiya a jiharsa zuwa jam'iyyar PDP, ya ce sun fice daga jam'iyyar APC ne saboda talauci da fatara tare da rashin adalci da ake yi a APC.

Wani gwani a Kudu ya tsine wa duk mai sauya jam'iyya zuwa APC

Wani gwani a Kudu ya tsine wa duk mai sauya jam'iyya zuwa APC
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

Legit.ng ta tattaro cewa basaraken ya ce shi da magoya bayansa sun koma jam'iyyarsu ta asali ne saboda yadda abubuwa suka tabarbare a jiharsa ta Edo. Ya ce gwamnatin APC bata tsinana komai ba a jihar har ma da tarayya.

Kalamansa: "Mun dawo gidanmu na asali wato PDP. Na tsinewa duk wanda ya biyo mu domin leken asiri domin daga baya ya koma jam'iyyar APC. Tsinuwar zata fada kan duk wanda ya koma APC. Munyi hannun riga da APC kuma ba zamu sake komawa jam'iyyar ba.

"Na tsinewa duk wanda ya koma APC. Babu wata cigaba da aka samu illa talauci. Mun dawo PDP saboda mu hada hannu da karfe mu gyra ta fiye da yada ta ke a baya."

Tsohon jigon na jam'iyyar APC ya ya tir da yadda jam'iyyar ta rika sakawa wadanda suka taimaka mata. Ya ce bayan sun taimakawa jam'iyyar tayi nasara a zaben gwamna da ya gabata. Abin farko da gwamna Godwin Obaseki ya yi shine jefa wasu magoya bayansa kurkuku ya kuma rsuhe gidajensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel