Zan inganta tattalin arzikin Najeriya da ganyen tabar wiwi – Dan takarar shugaban kasa

Zan inganta tattalin arzikin Najeriya da ganyen tabar wiwi – Dan takarar shugaban kasa

Omoyele Sowore, daya daga cikin masu burin yin takarar neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019, ya ce zai mayar da Najeriya daya cikin manyan kasashen duniya dake fitar da ganyen tabar wiwi.

Sowore, shugaban kamfanin yada labarai na SaharaReporters, ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo dake yawo a dandalin sada zumunta. Sai dai ba a bayyana ko yaushe ne Sowore ya saki faifan bidiyon ba.

Zan inganta tattalin arzikin Najeriya da ganyen tabar wiwi – Dan takarar shugaban kasa

Omoloye Sowore
Source: Depositphotos

A cikin bidiyon, Sowore, y ace ana noman ganyen tabar wiwi mafi kyau a duniya a jihar Ekiti, sannan ya kara da cewar kasashen duniya na samun biliyoyi daga saya ko sayar da ganyen tabar wiwi.

DUBA WANNAN: Kasar China na bin kowanne dan Najeriya bashin N15,000 - Rahoton bincike

Ya kamata mu fara bawa noman tabar wiwi muhimmanci ta yadda zamu ke samun kudin shiga daga saya ko sayar da ita kamar yadda wasu kasashen duniya ke samun biliyoyi daga kasuwancinta. Muna da ganyen tabar wiw mai kyau da ake nomawa a jihar Ekiti,” a cewar Sowore.

Sannan ya cigaba da cewar, “zan sanar da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) cewar zamu ke noman ciyawar wiwi domin fitar da ganyenta zuwa kasashen duniya da suke amfani das hi domin yin magunguna.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel