Wayar wa mutane kai akan kanjamau shine mafita – Aisha Buhari

Wayar wa mutane kai akan kanjamau shine mafita – Aisha Buhari

- Aisha Buhari ta yi kira ga kungiyoyi da su kara mayar da hankali wurin yawaita tunatar da mutane game da kanjamau

- Tayi wannan kira ne a kasar China

- Uwargidan shugaban kasar tace hakan ya zama wajibi ganin cewa matasa sun fi fadawa hadarin kamuwa da kuma yada cutar

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta yi kira ga kungiyoyi da su kara mayar da hankali wurin yawaita tunatar da mutane game da cuta mai karya garkuwar jikin dan adam wato Kanjamau akai-akai.

Aisha ta yi wannan kira ne a taron tsara hanyoin wayar da matasa akan cutar kanjamau a kasashen yankin Afrika da China wanda uwargidan shugaban kasar China, Peng Liyuan ta shirya.

Wayar wa mutane kai akan kanjamau shine mafita – Aisha Buhari

Wayar wa mutane kai akan kanjamau shine mafita – Aisha Buhari
Source: Facebook

A cewar uwargidan shugaban kasar aikata hakan ya zama wajibi ganin cewa matasa sun fi fadawa hadarin kamuwa da kuma yada cutar.

Peng Liyuan ta jinjina wa kokarin da kasashen yankin Afrika suka yi wajen ganin mutanen dake dauke da cutar sun sami magani da kare yara kanana daga kamuwa da cutar.

KU KARANTA KUMA: 2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari

Aisha Buhari dai na cikin tawagar da suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rakiya zuwa kasar China domin halartan taron kulla alaka tsakanin China da Afrika wadda ya gudana a farkon watan nan na Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel