Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan Mutane 9 da jikkatar 5 a jihar Kano

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan Mutane 9 da jikkatar 5 a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tabbacin ta kan salwantar rayukan mutane 9, yayin da biyar suka jikkata a sanadiyar aukuwar annoba ta ambaliyar ruwa cikin kananan hukumomi 9 dake fadin jihar kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Shugaban hukumar bayar da agaji reshen jihar, Alhaji Isa Bashir, shine ya bayyana yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin jihar a ranar Larabar ta da ta gabata.

Alhaji Bashir yake cewa, wannan annoba ta yi sanadiyar asara ga kimanin mutane 4, 475 cikin kananan hukumomi 9 da ta auku a fadin jihar ta Kanon Dabo.

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan Mutane 9 da jikkatar 5 a jihar Kano

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan Mutane 9 da jikkatar 5 a jihar Kano
Source: Twitter

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu rayukan mutane biyar sun salwanta cikin karamar hukumar Rimin Gado, uku a karamar hukumar Gabasawa da kuma daya-daya daga kananan hukumomin Getso da Gwarzo.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari da Mataimakin sa sun yi sabani kan batun 'Yan sanda jiha

A cewar sa, hukumar ta kammala kididdiga akan ta'adi gami da asara da wannan annoba ta yi sanadi cikin kananan hukumomi 9 yayin da ta ci gaba da kididdigar cikin sauran kananan hukumomin da ta auku a fadin jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta bayar da cikakken bayani dangane da wannan annoba da zarar ta kammala bincike gami da kididdigar ta cikin yankunan da ta auku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel