ASUU na sake gargadin komawa yajin aiki a jami'o'in kasar nan

ASUU na sake gargadin komawa yajin aiki a jami'o'in kasar nan

- Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'ar Ambrose Alli suna barazanar tafiya yajin aiki

- Sunyi koken rashin kwamitin shugabanci a jami'ar

- Rashin isasshen kudi don kula da jami'ar shima dalili ne na yajin aikin

ASUU na sake gargadin komawa yajin aiki a jami'o'in kasar nan

ASUU na sake gargadin komawa yajin aiki a jami'o'in kasar nan
Source: Depositphotos

Kungiyar Malamai masu koyarwa na jami'ar Ambrose Alli suna barazanar tafiya yajin aiki a sakamakon rashin zaben kwamitin shugabanci a jami'ar da rashin kudi don tafiyar da al'amuran jami'ar.

Kungiyar tace rashin kwamitin shugabanci yasa al'amuran jami'ar tafiyar Hawaii ya.

Shugaban kungiyar, Farfesa Monday Igbafen, ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai akan rashin cigaban dake fuskantar jami'ar.

Farfesa Igbafen yace kungiyar ta rubuta wasika babu adadi ga gwamna Godwin Obaseki akan bukatar kwamitin shugabancin jami'ar.

DUBA WANNAN: Da aka zo kama shi ya tsunduma ruwa

Ya nuna matsalar doka, kudade da kuma zartarwar karshe wacce ke bukatar kwamitin shugabancin jami'ar ta sa hannu sun tsaya tun a watan Augusta na 2017.

Farfesan yace ma'aikatan jami'ar basu samu cikakken albashin su na watanni hudu.

Yace rashin tallafin kudi daga gwamnatin jihar yasa basa iya zartar da manyan aiyuka a jami'ar.

Kungiyar mu ta yi duk abinda ya dace, gurin sanar da Gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki da sukan kawo ma jami'ar ziyara gurin nuna musu halin da jami'ar take ciki. Don haka ne muka yanke hukuncin zuwa yajin aiki, wanda bamu sa ranar dawowa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel