An kama iyaye da suka bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40

An kama iyaye da suka bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40

- Hukumar yan sandan Reedsburg da ke Wisconsin, US sunyi caraf da wasu yan Najeriya

- Yunwa ce tayi ajalin Ayanfe, sakamakon azumin kwana arba'in da yayi

- Yan sandan basu samu wani abinci a gidan ba

An kama iyaye da sukia bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40

An kama iyaye da sukia bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40
Source: Depositphotos

An kama iyaye da sukia bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40

An kama iyaye da sukia bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40
Source: Twitter

Hukumar yan sandan Reedsburg da ke Wisconsin a US, ta cafke Titilayo da Kehinde Omosebi, yan kasar Najeriya bayan da dansu Ayanfe ya mutu har lahira sakamakon azumin kwana arba'in da yayi.

A binciken da yan sandan suka je yi gidan su, bayan da Mista Kehinde yaje ya sanar dasu mutuwar danshi, sun tarar da gawar Ayanfe da shekaru 15 a rame,da Dan shekaru 11 shima a rame amma da ranshi, sai kuma Titilayo, mai shekaru 48 a duniya, itama a kanjame.

Mahaifin, Kehinde wanda ya bayyana kanshi a matsayin malamin addini a Cornerstone Reformation,yace iyalin shi sun fara azumin ne tun ranar 19,ga watan yuli, 2018 kuma zasu kai kwana arba'in sukayi.

DUBA WANNAN: Ya hallaka kansa da a kama shi

Jami'an basu tarar da abinci a gidan ba. A take suka kwashe su zuwa asibiti, inda Titilayo taki bada damar a duba lafiyar ta, ta hanyar danganta hakan da addini.

Dan shekaru 11, yana karbar taimako daga likitocin asibitin yankin Reedsburg, inda gawar Ayanfe take. Za a fara gudanar da bincike akan gawar a ranar litinin mai zuwa.

A halin yanzu Kehinde da Titilayo suna garkame a gidan kaso na Sauk inda ake tuhumar su da Wulakantar da yaro, wanda ya jawo mutuwa daya da kuma rashin lafiyar guda.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel