Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku ya soki Gwamnatin APC

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku ya soki Gwamnatin APC

Kun samu labari cewa maganar sauya fasalin kasa ta sa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da kuma Atiku Abubakar musayar kalamai a makon nan inda har Atiku ya nemi Osinbajo ya daina boye-boye game da matsayar sa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku ya soki Gwamnatin APC

'Dan takarar Shugaban Kasa Atiku yace Gwamnatin Buhari ba ta da kula
Source: Facebook

Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana yadda Gwamnatin Buhari ta kawo tsare-tsaren da su ka taimakawa al’ummar Najeriya. Sai dai Atiku Abubakar ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari tayi sanadiyyar rashin aiki da-dama.

Atiku Abubakar ya tunawa Yemi Osinbajo cewa a cikin watanni 21 rak ne mutum sama da miliyan 7 su ka rasa abin yi a Gwamnatin Buhari. Atiku yayi kaca-kaca da Osinbajo wanda yace a matsayin sa na Farfesa ya kamata ya san wannan.

KU KARANTA: Akwai mutanen da ake zargi da satar dukiyar Gwamnati a tafiyar Buhari

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya kuma yi tir da bashin Dala Miliyan 328 da Gwamnatin Buhari ta karbo a Kasar China a lokacin da wata Kasar waje ta dawowa Najeriya da Dala Miliyan 322 amma ta rabawa Talakawa.

Mataimakin Shugaban kasar a lokacin Obasanjo yace Najeriya ta ga bunkasar tattalin arziki a lokacin su na mulki. Atiku yace a wancan lokaci, Najeriya ta biya bashin fiye da Dala Biliyan 30 da ake bin ta duk da rashin kudi a sa’ilin.

Atiku ya nuna cewa kudin da aka samu a lokacin Obasanjo bai wuce daya-bisa-uku na abin da aka samu a Gwamnatin nan ta Buhari ba. Atiku yace idan aka bi lissafin Osinbajo, Gwamnatin Buhari ta samu Dala Biliyan 120 daga fetur.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel