Atiku ya fadawa Osinbajo ya tsaya wuri guda game da batun yi wa kasa garambawul

Atiku ya fadawa Osinbajo ya tsaya wuri guda game da batun yi wa kasa garambawul

Maganar da ake ta yi na sauya fasalin Najeriya ya jawo ana maidawa juna kalamai tsakanin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinabajo da kuma Atiku Abubakar inda Atiku ya nemi Osinbajo ya bayyanawa kowa matsayar sa.

Atiku ya fadawa Osinbajo ya tsaya wuri guda game da batun yi wa kasa garambawul

Atiku ya caccaki Mataimakin Shugaban kasa Osinabajo
Source: Depositphotos

Atiku Abubakar ya sha alwashin yi wa Najeriya garambawul idan ya samu mulki, wannan ya sa har Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ba sa amsa kwanakin baya inda yace Atiku bai san takamaiman abin da yake fada ba.

Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban na Najeriya ya sake yin jawabi inda ya bayyana abin da yake nufi. Atiku yace idan ya samu mulki zai yi kokari wajen yi wa Najeriya garambawul yana mai kawo matakai har 6 da zai dauka.

Daga ciki akwai karawa Jihohi karfin iko tare da takurawa Gwamnatin Tarayya. Atiku yace idan kuma ya samu mulki zai saida kayan da su ka zama alakakai ga Najeriya. Haka-zalika, Atiku yace zai bar kasuwa ya rika tsaida farashi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari da Osinbajo sun yi sabani kan wani batu

Atiku Abubakar yace ba zai bari a rika amfani da Jihar da mutum ya fito ba idan ya samu mulki. Atiku yace da zarar ya zama Shugaban Kasa, za a koma la’akari da Jihar da mutum ya fito. Atiku yana sa ran samun tikitin PDP a 2019.

Bugu da kari kuma ‘Dan takarar Shugaban kasar yace zai sa hannu a dokar da za ta canza harkar man fetur a kasar nan da zarar ya samu mulki. Tun 1995 dai Atiku yake kira a sakewa Najeriya garambawul idan ba ku manta ba.

Atiku Abubakar ya nunawa Farfesa Yemi Osinabajo cewa Gwamnatin APC tayi sanadiyyar rashin aikin yi ga mutane kusan miliyan 8 a Najeriya duk da kokarin ta na samawa mutum kusan 500, 000 abin yi cikin shekaru 3 a mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel