Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yanki fam din takaran shugaban kasa a APC

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yanki fam din takaran shugaban kasa a APC

- Shugaba Muhammadu Buhari ya mallaki fam din takara a zabe mai zuwa

- Wata kungiyar magoya bayansa ne suka yankar masa fam din

- An yanki fam din akan naira miiyan 45

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanki fam din nuna ra’ayin tsayawa takaran kujerar shuaban kasa a zabe mai zuwa karkashin jam’iyyarsa All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Kungiyar magoya bayan shugaban kasar mai suna Nigerian Consolidation Ambassadors Network ce ta siya fam din a madadin shugaban kasar a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yanki fam din takaran shugaban kasa a APC

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yanki fam din takaran shugaban kasa a APC
Source: UGC

Shugaba Buhari dai na chan kasar China inda ya ke halartan taron China da Afrika a lokacin da wannan abun alkhairi ya riske shi.

An dai siya masa fam din ne akan farashin da uwar jam’iyya ta nuna ra’ayin siyar da fam din dan takara wato naira miliyan 45.

Za’a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya ne a watan Fabrairun shekara mai zuwa wato 2019.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan tat ace za’a samar dad an takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct”kenan a turance.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel