Kasar China na bin kowanne dan Najeriya bashin N15,000 – Rahoton Bincike

Kasar China na bin kowanne dan Najeriya bashin N15,000 – Rahoton Bincike

- Najeriya ta ciyo bashin tiriliyan N3tn daga kasar China a cikin shekara hudu da suka gabata

- Wani rahoton bincike ya ce idan aka raba wa mutanen Najeriya, miliyan 198, Naira tiriliyan N3tn kowa zai samu N15,000

- Rahoton ya kara da cewar kasar China na kokarin kwace ragamar sarrafa tattalin arzikin Afrika daga hannun Amurka da Turai

Najeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan N3tn daga kasar China a cikin shekara hudu da suka gabata. Gwamnatin Najeriya ta ciyo bashin ne a jimka biyu; dalar Amurka biliyan $3.1bn a shekarar 2014 da kuma biliyan $6bn domin aiyukan raya kasa a cikin shekara uku da suka gabata, kamar yadda mai nazarin siyasa Theophilus Abba ya fada.

Wannan adadin (Tiriliyan N3trn) bai hada da sabon yarjejeniyar ciyo sabon bashin dalar Amurka biliyan $60 da shugaba Buhari da takwaransa na China, Xi Jin Pin, suka saka a hannu a kai ba a cikin satin nan a birnin Beijin.

Kasar China na bin kowanne dan Najeriya bashin N15,000 – Rahoton Bincike

Buhari a kasar China
Source: Twitter

A lissafin gwari-gwari, idan raba tiriliyan N3tn, bashin da kasar China ke bin gwamnatin Najeriya, da adadin mutanen Najeriya, miliyan 198, kowa zai samu N15,000, kwatankwacin mafi karancin albashi a Najeriya.

Rahoton ya kara da cewar kasar China na kokarin kwace ragamar sarrafa tattalin arzikin Afrika daga hannun Amurka da Turai.

DUBA WANNAN: 2019: Matasa sun fara hada kudi domin sayawa Buhari fam din takara

Yanzu haka kasashen Afrika da suka hada da Liberia, Ghana, da Angola na amfana da bashin da kasar China ke kwararowa nahiyar.

Wasu masu nazarin siyasa na ganin cewar akwai hatsari a irin wannan bashin da kasar China ke antayawa kasashe masu tasowa tare da bayyana cewar wata hanya ce da kasar China zata shigo da salon mulki da tafiyar da gwamnati irin nata a kasahen Afrika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel