Wasu da ake zargi da laifin sata da ke tare da Shugaba Buhari a APC

Wasu da ake zargi da laifin sata da ke tare da Shugaba Buhari a APC

Yanzu haka Shugaba Muhammadu Buhari ya shiryawa tsaya takarar Shugaban kasa a 2019. Akwai wasu manyan ’Yan siyasa da ake zargi da satar fiye da Biliyan 200 da ke goyon bayan Shugaban kasar a halin yanzu.

Wasu da ake zargi da laifin sata da ke tare da Shugaba Buhari a APC

Akwai wasu da ake wa shaidar sata a bayan Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Jaridar Punch ta kawo jerin wadansu mutane da ake zargi da satar kudin cikin masu goyon bayan tazarcen Shugaban kasar.Wadannan ‘yan siyasa da su ka sha alwashin ganin Buhari ya zarce sun hada da Sanatoci irin su Abdullahi Adamu; Aliyu Wamakko.

Daga cikin wannan jeri akwai Sanata Godswill Akpabio, da kuma irin su tsohon Gwaman Orji Uzor Kalu. Sauran wadanda ake zargi ko tuhuma kuma sun hada da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal.

Minista Rotimi Amaechi; Gwamna Abdulaziz Yari; da kuma Ali Modu Sheriff su na cikin wannan jeri.

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya soki Buhari

Ga ‘Yan siyasa 3 da ke kan gaba wajen irin wannan zargi:

1. Abdullahi Adamu

Ana zargin Sanatan na Nasarawa Abdullahi Adamu da satar sama da Naira Biliyan 15 lokacin yana Gwamnan Nasarawa. Yanzu haka yana cikin ‘Yan gaban goshin Buhari a Majalisa.

2. Aliyu Wamakko

Sanata Aliyu Wamakko ne Jagoran yakin neman zaben Buhari a 2019. Shi ma dai Sanatan yana da bayanin da zai yi a gaban Hukumar EFCC na satar Biliyan 15 a Sokoto.

3. Godswill Akpabio

Ana zargin tsohon Gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio da laifin satar fiye da Biliyan 100 daga asusun Jihar sa lokacin yana Gwamna. Yanzu dai Sanatan ya koma APC.

Shi kuwa Ministan sufuri wanda shi ne Sarkin yakin neman zaben Shugaba Buhari a 2015 yana da kashin satar Biliyan 97 a kan sa. Har yanzu dai Hukumar EFCC ba ta soma binciken sa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel