Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta biya masa naira miliyan 45 kudin takara

Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta biya masa naira miliyan 45 kudin takara

Wata kungiyar magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna ‘National consolidation Ambassadors Network’ ta shiga sawun gaba wajen nuna ma Buhari ana mugun tare.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba 5 ga watan Satumba ne yayan wannan kungiyar yan kishin kasa ta yi ma babban ofishin jam’iyyar APC tsinke dake babban birnin tarayya Abuja, inda suka gana da shugaban jam’iyyar, Adams Oshimole.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi raddi ga Atiku bisa bakar maganar daya fada akan Buhari

Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta biya masa naira miliyan 45 kudin takara

Takardar shiga takarar Buhari
Source: Facebook

A yayin ganawarsu da shugaba Oshiomole, kungiyar ta bakin shugabanta Sunusi Musa ta bayyana masa burinta na sayan ma shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar takara da zata bashi damar sake tsayawa takarar shugaban kasa karo na biyu.

Jim kadan bayan gabatar da jawabinsa, sai Barista Sunusi Musa ya mika ma shugaban jam’iyyar shaidar karbar kudi a banki na naira miliyan arba’in da biyar (N45,000,000), farashin sayan takardar kenan ga masu sha’awar takarar shugaban kasa.

Idan za’a tuna a yan kwanakinnan wasu bayanai na kanzon kurege na yawo a kafafen sadarwar zamani na cewa wai shugaba Buhari yace bashi da halin da zai iya biyan naira miliyan 53 kudin yankan fam na shiga takara, sai dai ba gaskiya bane.

Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta biya masa naira miliyan 45 kudin takara

Kudin
Source: Facebook

A ranar Talata ne shugabancin jam’iyyar APC ta kasa ta fitar da sanarwar farashin yankan fom ga dukkanin masu takarar mukamai daban daban a karkashin inuwarta, inda ta sanya naira miliyan 45 ga masu takarar shugaban kasa sai kuma naira miliyan 25 ga masu takarar mukamin gwamna.

A wani labarin kuma har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari yana can kasar China inda ya kai ziyarar kwanaki biyu don halartar taron kulla dagantala tsakanin kasar China da kasashen Afirka karo na biyu, taron da ake sa ran zai amfanar da Najeriya da abubuwa da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel