Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS

Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS

- Sifeta Janar na rundunar yan sanda, ya gargadi jami'an FSARS da su kauracewa tsare mai laifi sama da awanni 48, ko su fuskanci hukuncin kora daga aiki

- Sifeta Janar Idris, ya bayyana hakan ne a shalkwatar rundunar yan sanda ta jihar Anambra da ke Amawbia, a taron bita da aka shiryawa jami'an hukumar

- Ya ce nn haramta ma jami'an hukumar, yin bincike a wayoyi ko na'ura mai kwakwalwa na mutanen da basuji ba basu gani ba

Sifeta Janar na rundunar yan sanda, Ibrahim Idris, ya gargadi jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya FSARS, da ke a fadin kasar, da su kauracewa tauye hakkin dan Adam, musamman tsare mai laifi sama da awanni 48, ko kuma su fuskanci hukuncin kora.

Idris wanda ya ce duk wani jami'in hukumar ta FSARS da ya ke ganin cewa ba zai iya bin dokokin da aka shimfidawa aikin ba, to ya kama gabansa.

Ya ce: "daga yanzu duk wani jami'in FSRARS da aka kama da tsare mai laifi sama da awanni 48 ba tare da kai shi kotu ba, zai fuskanci hukuncin kora daga aiki."

Sifeta Janar Idris, ya bayyana hakan ne a shalkwatar rundunar yan sanda ta jihar Anambra da ke Amawbia, a taron bita da aka shiryawa jami'an hukumar ta FSARS.

KARANTA WANNAN: Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi

Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS

Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS
Source: Depositphotos

Da ya samu wakilcin kodinetan rundunar X-Squad na kasa, Mr. Amaechi Elumelu, wanda kuma mataimakin kwamishinan yan sanda ne, Sifeta Janar ya ce an samar da hukumar FSARS don dakile fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

"An kirki wannan hukumar taku ne don dakile fashi da makami da garkuwa da mutane, ba wai don wani aiki bayan wannan ba.", a cewar Idris.

Ya ce bayan sake fasalin da akayiwa hukumar tsaro ta fararen kaya, an bukaci dukkanin jami'an hukumar da su gudana da bincike kan lafiyarsu, musamman bangaren kwakwalwa da karfin tunani, inda ya kara da cewa an samar da sashen tuntuba da shawarwari a cikin hukumar.

KARANTA WANNAN: Malaman makaranta da na kiwon lafiya 2,000 suka mutu a shiyyar Arewa maso Gabas

Ya kara da cewa: "An haramta maku binciken wayoyi ko na'ura mai kwakwalwa na mutanen da basuji ba basu gani ba, har sai idan an baku izinin hakan daga Sifeta Janar ko wani babban jami'i da aka bashi ikon yin hakan.

"An haramta maku tsare mai laifi sama da wanni 48 ba tare da kun kaishi kotu ba"

Ya ce an samar da wani sashe a cikin hukumar da zai rinka kula da adadin lokutan da masu laifi zasu rinka zama a hannun hukumar da kuma tattara bayanai na masu laifi don zuwa kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel