An damke wasu korarrun sojoji da suka sace motar gingimari

An damke wasu korarrun sojoji da suka sace motar gingimari

- Jami'an 'yan sanda sun kama wasu korarrun sojoji da suka sace motar gingimari

- Daya daga cikinsu sojin kasa ne, dayan kuma jami'in sojan saman Najeriya ne

Jami'an 'yan sanda a Legas sun kama wasu mutane biyar da suka sace motar gingimari makare da jarkokin man gyada da kudinsa ya kai N13.2 miliyan a babban titin Epe.

A sanarwar da hukumar ta bayar a yau Laraba, 'yan sandan sun ce anyi fashin ne a ranar 2 ga watan Satumban 2018.

Wadanda ake zargi da fashin sun hada da wani korarren soja; Akintola Abiodun da sojin sama da aka sallama daga aiki; Chidi Osegbu wanda ake samu shi da kayan soji na bogi har da katin sheda duk na bogin.

An kamo sojoji da suka sace motar gingimari saboda an kore su daga aiki

An kamo sojoji da suka sace motar gingimari saboda an kore su daga aiki
Source: Twitter

Sauran wadanda ake zargin sun hada da Monday Ayele da Esowanne Emeka.

Direban motar da aka yiwa fashi, Rabiu Kazeem, ya ce yana tahowa daga Ajah ne 'yan fashin suka tsayar dashi.

DUBA WANNAN: Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

"Muna isa Epe, wata motar sojoji da tsaya kusa da mu kuma wasu mutane sanya da kayan sojoji suka fito suka umurci in fita daga mota na, yaron mota na ya tsere cikin daji," inji Kazeem.

"Sun fitar da ni daga mota na da karfi kuma suka shiga cikin "motar su kayi gaba sai dai basu san cewa na makale a karkashin motar ba na bi su har zuwa Ikorodu road.

"Wani mai babur ya rika bin motar a baya kuma ya ya ce min in sauka daga motar zai taimake ni, a lokacin ban gane tare su ke ba.

"Da na lura ya tafiya a hankali sai na gane cewa tare suke, daga nan sai na sanar da mutanen da ke unguwar kuma nan take muka kira 'yan sanda suka kama 'yan fashin." inji Kazeem.

Bayan kama su, Ayele da Emeka sun amsa cewa su sojoji ne da aka kora daga aiki a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kwamishinan 'yan sandan Legas, Imohimi Edgal, ya ce idan an kammala bincike za'a gurfanar da su gaban kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel