Fadar shugaban kasa ta yi raddi ga Atiku bisa bakar maganar daya fada akan Buhari

Fadar shugaban kasa ta yi raddi ga Atiku bisa bakar maganar daya fada akan Buhari

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku ABubakar bisa wasu bakaken maganganu daya fada akan Buhari.

A wata hira da Atiku yayi da kamfanin dillancin labaru na AFP, ya bayyana fargabar ko Buhari zai bari ayi zabe na gaskiya a 2019, sa’annan ya bayyana Buhari a matsayin mutumin da baya tankwaruwa kuma mutum ne mayen mulki, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: APC ta Kano ya tabbatar da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

“Ba kamar Goodluck Jonathan ba wanda ya mika mulki a 2015 cikin ruwan sanyi, a yanzu muna magana ne akan tsohon janar na Soja, kuma mutumin da baya tankwaruwa, mayen mulki, wanda ba zai mika mulki cikin ruwan sanyi ba koda an kada shi.” Inji Atiku.

Fadar shugaban kasa ta yi raddi ga Atiku bisa bakar maganar daya fada akan Buhari

Atiku Buhari
Source: Facebook

Sai dai a cikin martanin da fadar shugaban kasa ta aika ma Atiku, tace tabbas Buhari mutum ne wanda baya tankwaruwa akan duk abinda ya shafi sata, almundahana, cin hanci da rashawa, amma batun Buhari mayen mulki ne ba gaskiya bane.

“Mun ji maganganun da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi game da Buhari, tuna Atiku ya fara amfani da sunan Buhari don samun takara a jam’iyyar da take cikin zaman makoki har yanzu tun bayan kayan da ta sha a zaben 2015, toh muna fada masa tabbas buhari baya tankwaruwa.

“Baya tankwaruwa akan duk wani abinda ya shafi satar kudaden al’umma da barnata dukyar kasa, Buhari baya tankwaruwa akan tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin gwamnati, baya tankwaruwa wajen ganin an gayara Najeriya, don haka yake yaki da rashawa ba sani ba sabo.” Inji sanarwar.

Haka zalika sanarwar data samu sa hannun kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ta bayyana Buhari a matsayin cikakken dan dimukradiyya, wanda yake mulki cikin tsafta tare da sadaukar da rayuwarsa ga jama’a, hakan ne ya say an Najeriya suka aminta da shi.

Daga karshe Adesina ya tabbatar ma Atiku Abubakar cewa babu wanda zai yi rigima akan mulki a shekarar 2019, “ba dai a mulkin Buhari ba, yan Najeriya ba fada suke so ba, sai dai mu ja hankalin wasu manyan mutane da su dinga tauna magana kafin su furtata.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel