2019: Tawagar yakin neman zaben Saraki sun isa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas

2019: Tawagar yakin neman zaben Saraki sun isa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas

Gabannin isowarsa yankunan arewa maso gabas da arwa maso yamma, tawagar yakin neman zaben shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki sun isa yankunan domin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Legit.ng ta tattaro cewa tawagar sun samu jagorancin Sanata Ubali Shittu (arewa maso yamma) da kuma Isa Hamma Misau (arewa maso gabas).

A cewar wata sanarwa daga kakakin Saraki, Yusufu Olaniyonu, tawagar zasu gudanar da tarurruka da dama a fadin jihohin arewaa maso yamma bakwai da jihohin arewa maso gabas shida.

2019: Tawagar yakin neman zaben Saraki sun isa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas

2019: Tawagar yakin neman zaben Saraki sun isa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas
Source: Facebook

Shugaban majalisar dattawan wadda ya bayyana kudirinsa na neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP a kwanakin baya ya gana da gwamnonin jihohi tara, wadanda suka hada da Nyesom Wike na Rivers, Seriake Dickson na Bayelsa; Udom Emmanuel na Akwa Ibom; Ifeanyi Okowa na Delta; Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu; Okezie Ikpeazu na Abia; Abdulfatah Ahmed na Kwara; da kuma Ayodele Fayose na Ekiti.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari

Ya kuma gana da tsoffin masu ruwa da tsaki na kasar da suka hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, Ibrahim Badamasi Babangida da dai sauransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel