Jam'iyyar PDP ta fara raba katin jam'iyyar ga mambobi 100,000 a jihar Sokoto

Jam'iyyar PDP ta fara raba katin jam'iyyar ga mambobi 100,000 a jihar Sokoto

- PDP a jihar Sokoto ta fara rabawa mambobinta 100,000 katin zama dan jam'iyyar don fuskantar zaben 2019

- Shugaban jam'iyyar na jihar Alhaji Ibrahim Milgoma, ya ce an kafa kwamitin mutane hudu a kowace karamar hukuma don nasarar raba katin

- Ya ce gwamnatin APC tun daga matakin kasa ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa yan Nigeria, don haka ne PDP zata yi galaba akanta

A ranar Larabar nan Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, ta fara rabawa mambobin jam'iyyar 100,000 katin shaidar zama cikakken dan jam'iyyar,tare da daukar alwashin samun nasara akan jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar.

Da ya ke zantawa da shuwagabannin jam'iyyar a matakan kananan hukumomi 23 na jihar Sokoto, shugaban jam'iyyar PDP na jiahr, Alhaji Ibrahim Milgoma, ya ce za'a raba katin ga mabobi 100,000 da ke a fadin jihar.

Ya ce an kafa kwamitin mutane hudu a kowace karamar hukuma na jihar, don tabbatar da nasarar raba katin ga mambobin jam'iyyar.

KARANTA WANNAN: Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi

Jam'iyyar PDP ta fara raba katin jam'iyyar ga mambobi 100,000 a jihar Sokoto

Jam'iyyar PDP ta fara raba katin jam'iyyar ga mambobi 100,000 a jihar Sokoto
Source: Depositphotos

Milgoma ya bayyana cewa da tsofaffi dama sababbin shiga jam'iyyar na da damar yin rijista a gundumominsu, inda ya kara da cewa za'a martabar kowane mamba ba tare da nuna bangaranci ba.

"Wannan shine karon farko da muka gudanar da taron masu ruwa da tsaki, tun bayan da gwamnan jihar Aminu Tambuwal ya bar APC ya koma PDP. A yanzu kawunanmu hade suke kuma babu wariyar kai balle nuna bangaranci tsakanin tsofaffi da sabbin shiga jam'iyyar.

"Mun kafa kwamiti a kowace karamar hukuma don tabbatar da nasarar raba katin ga mambobin jam'iyyar. A don haka, muna a shirye don samar da karin kati ga mambobi da zaran an kammala wannan rabon" a cewar sa.

Ya jaddada cewa PDP zata samu galaba akan APC a zaben gwamnan a 2019 na jihar. A cewarsa, gwamnatin APC tun daga matakin kasa ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa yan Nigeria, da wannan dalilin ne za'a sauketa daga mulki a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel