Yanzu Yanzu: Zan tsaya takarar kujerar majalisar dattawa - Amosun

Yanzu Yanzu: Zan tsaya takarar kujerar majalisar dattawa - Amosun

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya bayyana kudirinsa na tarar kujerar dan majalisar mai wakiltan Ogun ta tsakiya a majalisar dattawa.

Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Mitros Suites, Ibara, Abeokuta.

Amosun dai zai gama zangonsa na biyu kenan a matsayin gwamnan jihar Ogun karkashin inuwar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Yanzu Yanzu: Zan tsaya takarar kujerar majalisar dattawa - Amosun

Yanzu Yanzu: Zan tsaya takarar kujerar majalisar dattawa - Amosun
Source: Depositphotos

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan ta tace za’a samar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct” kenan a turance.

Ta kuma sanya zaben fidda gwani na gwamnoni zai gudana a ranakun Litinin, 24 ga watan Satumba da 25 ga watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel