Rikicin Shugabanci: Ko dai ayi gyara ko mu yaga lema - Dankwambo ya gargadi PDP

Rikicin Shugabanci: Ko dai ayi gyara ko mu yaga lema - Dankwambo ya gargadi PDP

- Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, ya gargadi jam'iyyar PDP akan nuna banbanci da ta ke yi tsakanin sabbin shigowa jam'iyyar da wadanda suka reneta

- Dankwambo ya ce idan har jam'iyyar ba ta canja salon tafiyar da shugabancinta ba, to babu abinda zai hana su yaga lemar kowa ma ya huta, ayi ba wan ba kanin.

- A ranar 4 ga watan Agusta, gwamnan jihar ta Gombe, ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar PDP

Daya daga cikin wadanda suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, kuma Gwamnan jihar Gombe, Alh. Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi kira da babbar murya ga jam'iyyar ta kasa, da ta daina nuna banbanci tsakanin sabbin shiga jam'iyyar da wadanda suka raini jam'iyyar.

Dankwambo ya ce: "Mune muka raini jam'iyyar har ta kawo wannan matakin da ta ke a yanzu, har ma ta zama abin sha'awar da wasu ke tururuwar shigowa cikinta, amma take-taken da jam'iyyar ke nuna na fitar da dan takarar shugabancin kasar a 2019 ga sabbin shigowa jam'iyyar abin takaici ne"

Gwamnan ya ce ko jam'iyyar ta farka daga barcin da ta ke yi, don zabar wadanda suka sadaukar da kudinsu, lokacinsu, iliminsu dama karfinsu wajen yiwa jam'iyyar hidima, ko kuma su yaga lemar kowa ma ya huta, ayi ba wan ba kanin.

KARANTA WANNAN: Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi

Rikicin Shugabanci: Ko dai ayi gyara ko mu yaga lema - Dankwambo ya gargadi PDP

Rikicin Shugabanci: Ko dai ayi gyara ko mu yaga lema - Dankwambo ya gargadi PDP
Source: Depositphotos

A baya bayan nan Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Agusta, gwamnan jihar ta Gombe, ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasar, inda ya ce hakan ya biyo bayan tarin kiraye kirayen da ya samu daga al'ummar Nigeria na tsayawa takarar.

Da yake bayyana wannan kudiri nasa a garin Gombe, dan takarar shugaban kasar ya ce zai maida hankali wajen farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar daga darajar Noma da kasuwanci da kuma yaki da yunwa da talauci da ta yiwa al'umar kasar katutu.

A wani labarin:

Rikici ya barke a cikin majalisar dokoki ta jihar Ogun a ranar Talata, bayan da majalisar ta yi watsi da shirin wasu mambobinta guda biyu na sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Rahotanni sun bayyana cewa yan majalisun biyu sun gaza tabbatar da cewa akawai rabuwar kai a cikin jam'iyyar APC kamar yadda suka bayyana a matsayin dalilinsu na sauya shekar.

KARANTA CI GABAN LABARIN >>> Majalisar dokoki a Ogun ta yi watsi da bukatar sauya shekar wasu yan majalisu zuwa PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel